ƙwayoyin cuta Coronaviruses na daga cikin wani babban rukunin da aka sani suke jawo cuta daga mura da aka fi sani zuwa cututtuka mafi tsanani kamar su cutar numfashi na gefen larabawa wato Middle East Respiratory Syndrome (MERS) da cutar hanyoyin numfashi mai tsanani wato Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS). An gano sabuwar cutar COVID-19 a shekarar 2019 a garin Wuhan na ƙasar China. Wannan sabuwar cutar coronabirus ce baʻa taɓa samun irinta a mutum ba. Wannan kwas ya bada gabatarwa zuwa cutar COVID-19 da sauran cututtukan hanyoyin numfashi da ke tasowa kuma an haɗa shi don ma'aikatan kiwon lafiya, masu gudanar da rahoton cututtuka da masu aiki a majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyoyi na duniya da masu zaman kansu NGOs. *Tunda an kafa sunan bayan an kirkiro abun, duk lokaci da aka ce nCoV yana nufin COVID-19, cutar da kwayar cutar coroabirus da aka gano ke jawo shi.*
Self-paced
Language: Hausa
COVID-19

Course information

Hakanan ana samun wannan karatun a cikin yaruka masu zuwa:

English - français - Español - 中文 - Português - العربية - русский - Türkçe - српски језик - فارسی - हिन्दी, हिंदी - македонски јазик - Tiếng Việt - Indian sign language - magyar - Bahasa Indonesia - বাংলা - اردو - Kiswahili - አማርኛ - ଓଡ଼ିଆ - Tetun - Deutsch - Èdè Yorùbá - Asụsụ Igbo - ਪੰਜਾਬੀ - isiZulu - Soomaaliga - Afaan Oromoo - دری - Kurdî - پښتو - मराठी - Fulfulde- සිංහල

Taƙaitaccen bayani: Wannan kwas na gabatar da bayani gabaɗaya akan ƙwayoyin cuta da suke fitowa, hadda sabin koronabirus. A ƙarshen kwas ɗin, ya kamata ka iya bayani akan:

 • Yanayin ƙwayoyin cuta da suke fitowa, yaya ake ganewa kuma yadda ake nazari akan ɓarkewa, dabarun kariya da kula da ɓarkewa sakamakon sabin ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi

 • Waɗanne irin dabaru ya kamata ayi amfani da su wajen sanarwa akan hatsarori da kuma shigar da al'umma domin ganewa, karewa da kuma taimakawa a lokacin fitowar sabuwar cutar hanyoyin numfashi.

Akwai kayayyaki da aka haɗa da kowane littafi da zai taimaka maka wajen karin ilimi akan wannan batu

Manufar koyon: Bada bayani akan asalin ƙaʻidojinkwayoyi cuta da suke fitowa da kuma ta yaya za a iya taimakawa idan ya barke.

Adadin Lokacin shirin: Kimanin awanni uku (3).

Takardar shaida: Babu takaddun shaida a wannan lokacin.

An fassara zuwa harshen Hausa daga Emerging respiratory viruses, including COVID-19: methods for detection, prevention, response and control, 2020. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ba ta da alhakin abin da ke ciki ko ingancin wannan fassara. Idan an sami rashin daidaito tsakanin Turanci da kuma fassarar Hausa, Turancin na ainihi shine zaʻa ɗauka a matsayin ingantacce.

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO bata tantance wannan fassarar ba. Wannan rubutu an shirya ne don taimakawa koyarwa kawai

Course contents

 • ƙwayoyin cuta masu fitowa, hadda COVID-19: Gabatarwa:

  Wannan takataiccen gabatarwan na bada bayanin akan ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa, hadda COVID-19.
 • Littafi A: Gabatarwa zuwa ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa hadda COVID-19:

  Manufar koyon gabadaya: Don iya bayani meyasa ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa, hadda COVID-19 ya zama barazana a duniya ma lafiyar ɗan adam.
 • Littafi B: Gane ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa, hadda COVID-19: Sa ido da gwaje-gwaje:

  Manufar koyon gabadaya: Don bayani akan yadda za a gano da binciken barkewar ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa
 • Littafi C: Sanarwa akan haɗari da Shigar da al'umma a ayyuka:

  Manufar koyon gabadaya: Domin bayani akan wadanne irin dabaru ya kamata ayi amfani da shi don sanar ma al'umma akan haɗari da shigar da su a aikin gane, hana da taimakawa ma COVID-19
 • Littafi D: Kariya da Taimako zuwa sabuwar kwayar cutar hanyoyin numfashi, hadda COVID-19:

  Manufar koyon gabadaya: Ɗon bayyana dabaru ma hana kula da ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi masu fitowa na gaggawa, hadda barkewar coronabirus.

Enroll me for this course

The course is free. Just register for an account on OpenWHO and take the course!
Enroll me now