Gabatarwa akan COVID-19: hanyoyin ganewa, kariya, taimakawa da kulawa

ƙwayoyin cuta Coronaviruses na daga cikin wani babban rukunin da aka sani suke jawo cuta daga mura da aka fi sani zuwa cututtuka mafi tsanani kamar su cutar numfashi na gefen larabawa wato Middle East Respiratory Syndrome (MERS) da cutar hanyoyin numfashi mai tsanani wato Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS).

An gano sabuwar cutar COVID-19 a shekarar 2019 a garin Wuhan na ƙasar China. Wannan sabuwar cutar coronabirus ce baʻa taɓa samun irinta a mutum ba.

Wannan kwas ya bada gabatarwa zuwa cutar COVID-19 da sauran cututtukan hanyoyin numfashi da ke tasowa kuma an haɗa shi don ma'aikatan kiwon lafiya, masu gudanar da rahoton cututtuka da masu aiki a majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyoyi na duniya da masu zaman kansu NGOs.

Tunda an kafa sunan bayan an kirkiro abun, duk lokaci da aka ce nCoV yana nufin COVID-19, cutar da kwayar cutar coroabirus da aka gano ke jawo shi.

Lura cewa abubuwan da ke cikin wannan kwas a halin yanzu ana sabunta su don nuna jagorar kwanan nan. Kuna iya samun sabbin bayanai kan wasu batutuwa masu alaƙa da COVID-19 a cikin darussa masu zuwa:

Alurar riga kafi: Tashar rigakafin COVID-19

Matakan IPC: IPC don COVID-19

Gwajin saurin gano cutar Antigen: 1) SARS-CoV-2 antigen fast diagnostic gwajin; 2) Mahimmin la'akari don aiwatar da SARS-CoV-2 antigen RDT

 • Lura: An sabunta waɗannan kayan a ƙarshe a ranar 16/12/2020.*
Self-paced
Language: Hausa
COVID-19

Course information

Hakanan ana samun wannan karatun a cikin yaruka masu zuwa:

English - français - Español - 中文 - Português - العربية - русский - Türkçe - српски језик - فارسی - हिन्दी, हिंदी - македонски јазик - Tiếng Việt - Indian sign language - magyar - Bahasa Indonesia - বাংলা - اردو - Kiswahili - አማርኛ - ଓଡ଼ିଆ - Tetun - Deutsch - Èdè Yorùbá - Asụsụ Igbo - ਪੰਜਾਬੀ - isiZulu - Soomaaliga - Afaan Oromoo - دری - Kurdî - پښتو - मराठी - Fulfulde- සිංහල - Latviešu valoda - తెలుగు -Esperanto - ภาษาไทย - chiShona - Kreyòl ayisyen -Казақ тілі - தமிழ் - Ελληνικά

Taƙaitaccen bayani: Wannan kwas na gabatar da bayani gabaɗaya akan ƙwayoyin cuta da suke fitowa, hadda sabin koronabirus. A ƙarshen kwas ɗin, ya kamata ka iya bayani akan:

 • Yanayin ƙwayoyin cuta da suke fitowa, yaya ake ganewa kuma yadda ake nazari akan ɓarkewa, dabarun kariya da kula da ɓarkewa sakamakon sabin ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi

 • Waɗanne irin dabaru ya kamata ayi amfani da su wajen sanarwa akan hatsarori da kuma shigar da al'umma domin ganewa, karewa da kuma taimakawa a lokacin fitowar sabuwar cutar hanyoyin numfashi.

Akwai kayayyaki da aka haɗa da kowane littafi da zai taimaka maka wajen karin ilimi akan wannan batu

Manufar koyon: Bada bayani akan asalin ƙaʻidojinkwayoyi cuta da suke fitowa da kuma ta yaya za a iya taimakawa idan ya barke.

Adadin Lokacin shirin: Kimanin awanni uku (3).

Takardar shaida: Akwai Tabbaci na Halarta ga mahalartan da suka cika aƙalla 80% na takardun kwas ɗin.

An fassara zuwa harshen Hausa daga Introduction to COVID-19: methods for detection, prevention, response and control, 2020. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ba ta da alhakin abin da ke ciki ko ingancin wannan fassara. Idan an sami rashin daidaito tsakanin Turanci da kuma fassarar Hausa, Turancin na ainihi shine zaʻa ɗauka a matsayin ingantacce.

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO bata tantance wannan fassarar ba. Wannan rubutu an shirya ne don taimakawa koyarwa kawai

Course contents

 • Rukuni na ɗaya 1: Kwayoyin cuta birus masu tasowa dake shafan hanyoyin numfashi:

  A karshen wannan rukunin, masu halartar zasu iya bayanin: yadda ƙwayoyin cuta suke tasowa, menene ƙwayoyin cuta koronabirus, su waye suka fi cikin haɗarin kamuwa da koronabirus, yadda zaka kare kanka
 • Rukuni na ɗaya 2: Ingantaccen sa ido da binciken bayyanar kwayoyin cututtukan numfashi:

  A ƙarshen wannan rukunin, mahalarta za su iya bayyana: Ƙara sanya idanu, Ydda za a gudanar binciken ɓarkewar cutar a mabanbantan wurare
 • Rukuni na ɗaya 3: Binciken ɗakin gwaje-gwaje :

  A karshen wannan rukuni, mahalarta yakamata zasu iya bayyana: da irin samfurori da ake buƙata, irin binciken dakin gwaje-gwajen da aka yi amfani da shi don tabbatar da cutar awanda ake zargi.
 • Rukuni na ɗaya 4: Sadarwa akan hatsarori:

  A ƙarshen wannan rukunin, ya kamata masu koyon za su iya: yi bayani akan muhimmar damuwa game da sadarwa akan hatsarorin bairos na cutar hanyoyin numfashi waɗanda suke ɓullowa, a ba da jerin aƙalla abubuwa uku waɗanda suka hana bin shawarwarin kiwon lafiya, da, gane muhimman hanyoyin tallafi domin aiwatar da sadarwa akan hatsarori a lokacin ɓarkewar cutar
 • Rukuni na ɗaya 5: Tattaunawa da Al'uma:

  A ƙarshen wannan rukunin, mahalarta za su iya: Yi bayanin a kalla dalilai uku da yasa masu bada taimakawa ke bukatar tattaunawa da al'uma yayin annoba, Bada jerin ƙalubalen da ake fuskanta a tattaunawa da al'uma (CE) da, Yi bayanin akan ingantaccen hanyoyin tattaunawa da al'uma wajen gano, kariya da ɗaukar mataki lokacin bullar annoba
 • Rukuni na ɗaya 6: Kariya daga kamuwa da Kuma kulawa (IPC) da kulawa a asibiti:

  A ƙarshen wannan rukunin, masu koyo zasu iya bayyana ƙa'idojin kariya daga kamuwa da cuta a cikin al'umma da kuma a wuraren kiwon lafiya.

Enroll me for this course

The course is free. Just register for an account on OpenWHO and take the course!
Enroll me now

Certificate Requirements

 • Gain a Confirmation of Participation by completing at least 80% of the course material.