课程进行中
ƙwayoyin cuta Coronaviruses na daga cikin wani babban rukunin da aka sani suke jawo cuta daga mura da aka fi sani zuwa cututtuka mafi tsanani kamar su cutar numfashi na gefen larabawa wato Middle East Respiratory Syndrome (MERS) da cutar hanyoyin numfashi mai tsanani wato Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS).
An gano sabuwar cutar COVID-19 a shekarar 2019 a garin Wuhan na ƙasar China. Wannan sabuwar cutar coronabirus ce baʻa taɓa samun irinta a mutum ba.
Wannan kwas ya bada gabatarwa zuwa cutar COVID-19 da sauran cututtukan hanyoyin numfashi da ke tasowa kuma an haɗa shi don ma'aikatan kiwon lafiya, masu gudanar da rahoton cututtuka da masu aiki a majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyoyi na duniya da masu zaman kansu NGOs.
Tunda an kafa sunan bayan an kirkiro abun, duk lokaci da aka ce nCoV yana nufin COVID-19, cutar da kwayar cutar coroabirus da aka gano ke jawo shi.
Lura cewa abubuwan da ke cikin wannan kwas a halin yanzu ana sabunta su don nuna jagorar kwanan nan. Kuna iya samun sabbin bayanai kan wasu batutuwa masu alaƙa da COVID-19 a cikin darussa masu zuwa:
Alurar riga kafi: Tashar rigakafin COVID-19
Matakan IPC: IPC don COVID-19
Gwajin saurin gano cutar Antigen: 1) SARS-CoV-2 antigen fast diagnostic gwajin; 2) Mahimmin la'akari don aiwatar da SARS-CoV-2 antigen RDT
Hakanan ana samun wannan karatun a cikin yaruka masu zuwa:
English - français - Español - 中文 - Português - العربية - русский - Türkçe - српски језик - فارسی - हिन्दी, हिंदी - македонски јазик - Tiếng Việt - Indian sign language - magyar - Bahasa Indonesia - বাংলা - اردو - Kiswahili - አማርኛ - ଓଡ଼ିଆ - Tetun - Deutsch - Èdè Yorùbá - Asụsụ Igbo - ਪੰਜਾਬੀ - isiZulu - Soomaaliga - Afaan Oromoo - دری - Kurdî - پښتو - मराठी - Fulfulde- සිංහල - Latviešu valoda - తెలుగు -Esperanto - ภาษาไทย - chiShona - Kreyòl ayisyen -Казақ тілі - தமிழ் - Ελληνικά
Taƙaitaccen bayani: Wannan kwas na gabatar da bayani gabaɗaya akan ƙwayoyin cuta da suke fitowa, hadda sabin koronabirus. A ƙarshen kwas ɗin, ya kamata ka iya bayani akan:
Yanayin ƙwayoyin cuta da suke fitowa, yaya ake ganewa kuma yadda ake nazari akan ɓarkewa, dabarun kariya da kula da ɓarkewa sakamakon sabin ƙwayoyin cutar hanyoyin numfashi
Waɗanne irin dabaru ya kamata ayi amfani da su wajen sanarwa akan hatsarori da kuma shigar da al'umma domin ganewa, karewa da kuma taimakawa a lokacin fitowar sabuwar cutar hanyoyin numfashi.
Akwai kayayyaki da aka haɗa da kowane littafi da zai taimaka maka wajen karin ilimi akan wannan batu
Manufar koyon: Bada bayani akan asalin ƙaʻidojinkwayoyi cuta da suke fitowa da kuma ta yaya za a iya taimakawa idan ya barke.
Adadin Lokacin shirin: Kimanin awanni uku (3).
Takardar shaida: Akwai Tabbaci na Halarta ga mahalartan da suka cika aƙalla 80% na takardun kwas ɗin.
An fassara zuwa harshen Hausa daga Introduction to COVID-19: methods for detection, prevention, response and control, 2020. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ba ta da alhakin abin da ke ciki ko ingancin wannan fassara. Idan an sami rashin daidaito tsakanin Turanci da kuma fassarar Hausa, Turancin na ainihi shine zaʻa ɗauka a matsayin ingantacce.
Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO bata tantance wannan fassarar ba. Wannan rubutu an shirya ne don taimakawa koyarwa kawai