Gabatarwa ga cutar kolera

Kwalara cuta ce da ke sa gudawa wanda ke faruwa ta cin abinci ko shan ruwa gurɓataccen mai ɗauke da kwayar cutar. Wannan karatun yana ba da gabatarwar gaba ɗaya game da kwalara kuma an tsara shi ne don ma'aikatan da suke bada taimako a lokacin ɓarkewa a cikin gaggawa mai tsanani ko cikin saitunan inda aka lalata ko rushe asalin gine-ginen muhalli.

**A lura: An samar da wannan kwas a 2017. Don sababbin abubuwa, a duba batutuwan kiwon lafiya da suka dace a kan Shafin yanar gizon WHO.

Self-paced
Language: Hausa
Cholera

Course information

Hakanan ana samun wannan karatun a cikin yaruka masu zuwa:

English - français - Português - العربية - Українська - Pashto - اردو - شاہ مُکھی

Bayanai a taƙaice: Cutar kwalara cuta ce mai saurin kamuwa wanda ke sa gudawa sakamakon hadiye gurɓataccen ruwa ko abinci. Wannan karatun yana ba da gabatarwar gaba ɗaya game da kwalara kuma an tsara shi ne don ma'aikatan da suke bada taimako a lokacin ɓarkewa a cikin gaggawa mai tsanani ko cikin saitunan inda aka lalata ko rushe asalin gine-ginen muhalli. Muna fatan cewa wannan karatun zai taimaka muku wajen sabunta abin da kuka riga kuka sani kuma zai taimaka muku wajen sauya kyayawan ka'idoji kan gudanar na kulawa na kwalara don aikata shi.

Manufofin koyo: A karshen wannan horon, mahalartar za su iya:

  • bayyana ma'ana da yanayin cutar kwalara da yadda ake gane barkewar ta;
  • bayyana ainihin hanyoyin da mutun yeke kamuwa da ita;
  • jeranta muhimman matakan kariya; da
  • bayyana yadda kula da kwalara ta kasance ta bangarori da yawa.

Tsawon Lokaci karatun: Kimanin awa ɗaya.

Takardar shaidar: Akwai Tabbaci na Halarta ga mahalartan da suka cika aƙalla 80% na takardun kwas ɗin.

An fassara zuwa harshen Hausa daga Cholera: Introduction, 2017. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ba ta da alhakin abin da ke ciki ko ingancin wannan fassara. Idan an sami rashin daidaito tsakanin Turanci da kuma fassarar Hausa, Turancin na ainihi shine zaʻa ɗauka a matsayin ingantacce. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO bata tantance wannan fassarar ba. Wannan rubutu an shirya ne don taimakawa koyarwa kawai.

Course contents

  • Gabatarwa zuwa kwalara:

    Wannan ɓangaren yana gabatar da takaitaccen bayani game da cutar.

Enroll me for this course

The course is free. Just register for an account on OpenWHO and take the course!
Enroll me now

Certificate Requirements

  • Gain a Confirmation of Participation by completing at least 80% of the course material.